Reverend Father Alia ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Benue
Aliyu Bello Mohammed, Katsina
Kwamitin zabe na zaben fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar APC a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ya bayyana Rev. Fr. Hyacinth Alia ne ya lashe zaben da aka sake gudanarwa a kananan hukumomi 11 na jihar.
Shugaban kwamitin zaben, Sanata Basheer Lado, wanda ya bayyana sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi, ya ce Rev. Fr. Alia ya samu jimillar kuri’u 219,002 inda ya doke wasu 11 da suka fafata a zaben.
A cewar shugaban kwamitin, tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Cif Micheal Aondoakaa ya samu kuri’u 606 yayin da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Barnabas Gemade ya samu kuri’u 450.
Sanata Lado ya kuma bayyana cewa tsohon Ministan Neja Delta, Dokta Sam Ode ya samu kuri’u 255 tare da dan majalisar wakilai, Hon. Herman Hembe ya samu kuri’u 688.
A wani sakamakon kuma, tsohon mataimakin gwamnan jihar Benue, Ochagu Steven Lawani ya samu kuri’u 120, Dr. Matthias Ibuan ya samu kuri’u 4,797, Farfesa Terhemba Shija ya samu kuri’u 219, Arc. Benard Yisa ya samu kuri’u 136 yayin da Mista Ayom Mlanga ya samu kuri’u 766 shi kuma Terwase Orbunde ya samu kuri’u biyu.
Sanata Basheer Lado ya bayyana cewa Rev. Fr. Alia ya samu mafi yawan kuri’u bayan da aka tattara sakamakon zaben kananan hukumomi goma sha daya a sake zaben da aka yi da na wasu goma sha biyu da jam’iyyar ta gudanar a baya don isa ga jimillar kuri’u.
Ya yabawa wakilan da suka halarci zabukan fidda gwanin kai tsaye bisa tsarin da suka nuna a yayin gudanar da atisayen, ya kuma bukace su da su rike jam’iyyar har sai an samu nasara a babban zabe.
Da yake mayar da martani kan sakamakon sake zaben da aka gudanar a wani taro na musamman, shugaban jam’iyyar APC na jihar Benue, Kwamared Austin Agada ya jaddada aniyar jam’iyyar na dawo da jihar Benuwe ci gaba daga rugujewa karkashin jagorancin jam’iyyar PDP.
Agada ya ce ya ga alamun nasara a jam’iyyar APC a jihar Benuwe tare da sake fitowa takarar Rev. Fr Alia a wurin taron.
A halin da ake ciki, kwamitin daukaka kara da shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka kafa zai fara zaman kwana daya a ranar Juma’a domin jin korafe-korafe daga ‘yan takarar da ke damun yadda za a gudanar da zaben fidda gwanin da aka sauya.
Leave a Reply