Gwamnan Jihar Anambara Chukwuma Soludo ya kaddamar da yakin neman zaben ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA a yankin Idemili ta Kudu da kuma kansilolin Anaocha , gabanin zabukan da za a gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris.
A yayin taron, Gwamnan ya kuma fara duba aikin gyaran hanyar Afor Nnobi-Awka Etiti-Ichida-Nkwo-Igboukwu, tare da kaddamar da aikin gina hanyar Nnokwa-Adazi Enu-Akwaeze mai tsawon kilomita 6.4.
Gwamnan ya nemi goyon bayan mutanen Anambara ga ’yan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, tare da ba da tabbacin ci gaba da samar da ribar dimokuradiyya ga jama’a.
Shuwagabannin kwamitin mika mulki na kananan hukumomin Idemili ta Kudu da Anaocha, Misis Amaka Obi da Mista Ikechukwu Ozor, sun bayyana dimbin ayyukan raya kasa da gwamnan ya yi a dukkanin sassan tattalin arzikin jihar, inda suka nuna cewa zaben APGA shine kuri’ar da za a ci gaba da samu.
A wuraren da ‘Yan takarar jam’iyyar APGA suka ziyarta, ciki har da Ikenna Iyiegbu, Sir Ejike Ikechukwu, Misis Njideka Oraedum, da dai sauran su, kuma sun yi alkawarin hada kai da Gwamnan don ci gaban jihar idan aka zabe shi.
Mambobin majalisar zartaswar jihar da suka hada da shugaban ma’aikata, Mista Ernest Ezeajughi, kwamishinan nishadi da al’adu, kwamishinan lafiya, Dr. Afam Obidike da kuma bangaren ayyukansu, Engr. Ifeanyi Okoma, dimbin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma masu aminci, suka halarci taron.
Leave a Reply