Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Accord, Farfesa Christopher Imumolen, ya ce ya kamata matasan Najeriya su tashi tsaye wajen zabar da matasa masu nagarta da kuma cancantar da za su tafiyar da al’amuran kasar.
Farfesa Imumolen ya bayyana hakan ne a Abuja babban birnin Najeriya yayin wata ganawa da manema labarai. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi imani da kan su, kada su yanke fatan shiga harkokin siyasa a kasar.
Farfesa Imumolen ya ce matasan Najeriya sun yi fice a ayyuka daban-daban na rayuwa, musamman a fannin siyasa da shugabanci, wasanni da kuma harkar nishadi.
Matashin mai shekaru 39 kwararre ne a fannin ilimi, kuma hamshakin dan kasuwa ya yi kira ga matasa da su rungumi harkokin shugabancin kasar nan da himma.
Ya yi nuni da cewa matasa masu shekaru ashirin da tara sun zama ministoci, tsohon shugaban Najeriya Janar Olusegun Obasanjo ya kasance shugaban kasa na soja yana da shekaru talatin da biyu.
Ya nanata cewa “muna nan ne domin mu wakilci matasan Najeriya, kuma a matsayinmu na dan takarar da ke wakiltar matasa a gasar, za mu iya yin hakan kuma mu tabbatar da hakan.”
“Idan matasa za su iya zama shugabanni a Grenada, idan matasa na iya zama Firayim Minista a Burtaniya, a Faransa, wasu ƙasashe to me yasa hakan ba zai iya faruwa a nan Najeriya ba?”
Ya bukaci da cewa “idan har za mu iya tallafawa ‘yan Najeriya ta kowane bangare na Najeriya to menene ya fi mu zama shugaban kasa da tafiyar da kasar nan.”
Dan takarar shugaban kasa na Accord ya yi zargin cewa “ dole ne matasan Najeriya su yi imani da kan su kuma su tafiyar da rayuwarsu tare, su gudanar da harkokin kasa gaba daya.
Ya kuma kalubalanci Matasan da su rika yiwa gwamnati hisabi “domin ganin mun dora gwamnati kan tabarbarewar tattalin arziki, sannan mu magance matsalar karancin man fetur da kuma matsalar kudi nan da makonni masu zuwa domin a yi adalci da kuma yadda za a shawo kan matsalar da sahihin zabe a Najeriya da shugabanni.
Leave a Reply