‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare sun gudanar da taro a kwalejin Wayne dake birnin Detroit a Amurka akan Zabukan 2023, karkashin jagorancin {Diaspora for good governance} wato yan Najeriya mazauna ketare masu sha’awar kawo shugabanci nagari, ya samu halartar wakilan wasu daga cikin manyan jamiyyun dake takarar kujerar shugabancin Najeriya a zabukan ranar 25 ga watan Febrerun da muke ciki.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki inda sauran al’umma suka shiga aka dama da su ta hanyar na’ura mai kwakwalwa a yanar Gizo daga sassan duniya baki daya wato Zoom.
Uwargida Omolara Abiodun Williams, ce ta wakilci dan takarar babbar jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party {PDP} Alh Atiku Abubakar. Professor Salewa Olafioye ya wakilci dan takarar jamiyya mai mulki ta All Progressive Congress {APC} Bola Ahmad Tinubu, inda shi kuma Mr Mike Okaka ya wakilci dan takara karkashin tutar jamiyyar Labour Party {LP} Mr Peter Obi.
Kowane wakili yayi bayanin irin shirye shiryen da dan takarar shi yake da su domin kawo sauyi kan yanayin zamantakewa, tattalin arziki, tsaro, samarwa da matasa ayyukan yi, ilimi da sauran su.
Da take gabatar da jawabin ta, wakiliyar jamiyyar PDP Omolara Williams ta bayyana dan takarar ta Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda “ya kware wajen harkokin jagorancin al’umma, ta la’akari da irin rawar da ya taka lokacin da yake mataimakin shugaban kasa daga shekarun 1999 – 2007 kuma zai yi amfani da wannan kwarewa wajen ceto kasar daga cikin halin da take ciki, ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki tare da kyautata yanayin tsaro a fadin kasar baki daya”.
“share matsalolin ‘yan Najeriya sai Alh Atiku Abubakar kasancewar sa dan kasa nagari mai kokarin hade kan jama’a, dan kishin kasa da ya kasance a shirye wajen kawo karshen matsalolin da suka yiwa kasar dabaibayi”, in ji Omolara.
A nasa jawabin Farfesa Salewa dake wakiltar bangaren APC da dan takarar ta Bola Ahmad Tinubu, bayyana nasa gwanin yayi “ ya sha gwagwarmaya domin tabbatar da mulkin demokradiyya a Najeriya saboda haka a bashi dama yana da matukar amfani kasancewar shi mai kudirin ganin mulkin demokradiyya ya samu gindin zama bama a Najeriya kadai ba, harma da nahiyar Africa baki daya shine ya dasa harsashen gina birnin Lagos na zamani da yanzu haka ya kasance birni na 6 mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Africa, saboda haka a bashi damar yin shugabanci zai dora kasar kan turba ta gari”.
Daukacin wakilan ‘yan takarkarun sunyi ta kokari wajen kare irin matakan da wadanda suke goyon baya zasu dauka wajen share wa ‘yan Najeriya irin manyan matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya ta da zarar sun dare Karagar mulki.
Wannan taro ya samu tagomashi inda jama’a suka dinga tura tambayoyin su kai tsaye ta hanyar na’urar zamani ana basu amsa.
Leave a Reply