Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa. Yemi Osinbajo ya sauka Badun ranar Juma’ a domin ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan takarar shi a zaben shugaban kasa a shekara ta 2023 karkashin Jamiyyar All Progessives Congress, APC.
Farfesa. Osinbajo ya isa Badun ne da misalin karfe 10.25 na safiyar Juma’ a a cewar hadiman shi.
Mataimakin Gwamnan jihar Oyo, Mr. Rauf Olaniyon, da wasu mambobin majalisar Jihar suka tarbe shi .
Daga filin jirgin sama tawagar ta wuce fadar sarkin Badun, Oba Lekan Balogun.
LADAN NASIDI
Leave a Reply