Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘ yan kasuwa da masu saka hannayen jari da su samar da hanyoyin da zasu kawo bunkasar tattalin arzikin kasa domin rage radadin talauci.
Ya kuma tabbatar wa ‘ yan kasuwar cewa gyaran albarkatu nauyin gwamnati ne.
Da ya karbi bakuncin Shugaban kanfanin Dangote company a fadar Shugaban kasa ranar Juma’ ,Shugaban yace kalubalen da suka shafi ban garen Sufuri da hasken wutar lantarki sune abubuwan dake kawo ci bayan hanyoyin kudaden shiga,saboda haka ya bukaci ‘ yan kasuwar kasar da ma Baki ‘ yan kasashen waje da sum aida hankali akan abubuwan da zasu kyautata rayuwar al’ umar kasa.
LADAN NASIDI
Leave a Reply