Take a fresh look at your lifestyle.

FADAR SHUGABAN KASA TAYI WATSI DA HANGEN NESA NA RUGUJEWAR NAJERIYA

0 162

Fadar shuagaban kasa tayi watsi da rade- raden da akayi bada jimawa ba na yiwuwar rushewar Najeriya

A cikin jawabin shi mai Magana da yawun fadar shugaban kasa, Garba Shehu, yace wannan harsashe ne da kasar Amurka tayi.

Shehu yace: A shekara ta 2005, wata mujallar Amurka “Harsashen rayuwar kasashen yankin sahara nan gaba” ta yada jita jitar yiwuwar hambaras da gwamnati da sojoji zasuyi a Najeriya. A wannan lokaci 2005 lokacin tsarin demokuradiya nada shekaru Shida da kamawa tun lokacin da bacha yayi juyin Mulki a shekara ta 1993,juyin mulkin soja na karshe.

Tun lokacin da farar hula ta koma tsarin demokuradiya a shekarar 1999 an gudanar da zabuka shida ,na shugaban kasa hudu.

 

Duk kuwa da sheidu hakar masu fadar hakan bata cimma ruwa baa.

 

Bada jimawa ba jakadan Amurka a Najeriya daga 2004-7 John Campbell ya yi wani rubutu inda yake cewa:

 

‘’Tunda ‘yan Najeriya sukayi ikirarin babu abunda zai samu kasar su,kazamin mulkin gwamnatin Shugaba  Goodluck Jonathan, barkewar kungiyar taadda ta boko haran,tashe tashen hankula a yankin Naija Delta kuma Arewa zata gane cewa  sun shiga wani hali na kakayi kayi”.

 

Sai gashi : a shekara ta 2015 mulkin Jonathan yasha kaye a zaben gama gari da ya baiwa Shugaba Muhammadu Buhari nasara.

 

“Campbell yana taka tsantsan akan sauran mutanen dake ganin rushewar Najeriya nan gaba. Hakan maganar take a koda yaushe babu abunda ya faru.Ban taba cewa nayi has ashen rugujewar Najeriya ba saboda nasan hakan ba zai taba yiwuwa ba. Amma inda hakan ya faru da an sanya al’ uma cikin wani hali na kakayi kayi .

 

Shehu ya tunatar da cewa Najeriya na nan daram.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *