Take a fresh look at your lifestyle.

YAKI DA SATAR DANYEN MAI: RUNDUNAR SOJIN RUWA TA SAMU NASARA

0 190

A aikin Operation DAKATAR DA BARAWO (OPDDB) da rundunar sojan ruwa ta kaddamar a Najeriya, rundunar ta dukufa ainun wajen yaki da barayin mai domin karya tattalin arzikin kasa ta samu nasarori da dama wajen yaki da barayin kuma kama barayi da kwace man da suka  sata.

 

A cikin jawabin shi, mai Magana da yawun rundunar sojan ruwa, Komodo Aoayo-Vaughan wanda ya sanar da haka a babban birnin tarayya Abuja yace “Jirgin ruwa Na Najeriya (NNS) DELTA a Warri, ya lalata wata haramtacciyar masanaantar sarrafa danyen mai dake gabar ruwa”.

 

Vaughan Yace jirgin IRS nada rumbunan ajiyar mai 16 ,manyan ramuka 3 da aka ajiye lita 500,000 a haramtacciyar hanyar sarrafa bakin mai, har da wajen da aka ajiye lita 700,000 da aka sata, Janareto da naurar tura mai guda hulu 4 . haka kuma an kama ovun 6 da ake dafa danyen mai a wari,wajen ajiye mai 12 da manyan ramukan da aka buye danyen mai da Gas.

 

A wata sabuwa kuma an kai hare hare ta jirgin sama a jhar Bayelsa a ranar 18 a ranar 19 ga watan Afrilu 2022 tare da harin gabar kogi a karamar hukumar Brass.

 

Haka kuma an kama manyan ovun 7 na dafa mai, tankin ajiyar mai guda 10  inda suke sarrafa Gas da Fetur.

 

Yace “an gano IRS a bakin kogin Lelemu dake kudu maso yammacin Warri ”.

 

Yace haka kuma an lalata manyan dakunan sarrafa man fetur,Gas da rumbun ajiyar main a karfe gudu 26 250,000litres of suspected stolen crude oil and 50,000litres of  illegally refined AGO were destroyed.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *