Hukumar yaki da sha ,Fatauci da Tuammali da Miyagun Kwayoyi ta kasa, NDLEA ta samu nasarar cafke babbandan kasuwar kwaya kuma biloniya Chif Afam Mallinson Emmanuel Ukatu wanda shine kashin bayan safarar kwayar tramadol na kimanin Naira biliyon uku da ya lakanta abun datawagar tsohon babban dan Sandan nan, Abba Kyari.
A cikin wata sanarwa Daraktan yada labarai na hukumar NDLEA a Abuja Mr Femi Babafemi said, “bayan watanni ana gudanar da bincike da sanya ido kafin a kama, Ukatu wanda shine shugaban kanfanin Mallinson Group aka kama shi da da lokacin da zai shiga jirgin sama akan hanyar shi ta zuwa Abuja dake filin jirgin saman Murtala a Legas ranar Laraba 13 ga watan Afrilu.”
“Bincike ya nuna cewa akasarin dimbin kayan maye daban daban da kuma kwayar Tramadol,duk haramtattu suna da alaka da kanfanin sarrafa magunguna na Ukatu,wadanda yake bad da sawu yana shigowa da su Najeriya.”
“Kana yana da kuma a asusun ajiyar kudi guda 103,da yake kuma anfani da su wajen gudanar da haramtacciyar sanaar shi.” A cewar Sanarwar.
LADAN NASIDI
Leave a Reply