Take a fresh look at your lifestyle.

Zan Maida Hankali Wajen Inganta Fannin Ilimi Da Rayuwar Matasa : Jimkuta

Musa Aminu, Abuja.

0 304

Yayin da ake kara tunkarar babban zabe a Najeriya, an bukaci matasan kasar da su guji shiga bangan siyasa domin kaucewa fadawa cikin halin da na sani.

Dantakarar kujerar majalisar dattawa a mazabar Jihar Taraba ta kudu dake Arewa maso gabashin Najeriya, Mr Devid Jimkuta shi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja fadar Mulkin Najeriya.

Devid Jimkuta ya bayyana cewa abun taikaci ne kwarai matuka idan akayi la’akari da yadda wadansu miyagun yan siyasa ke yin amfani da matasa ta hanyar da bata dace ba domin cimma wasu kebabbun manufofinsu, adon haka ya shawarci matasan da su kasance masu kauracewa duk wani ko wata dake da aniyyar yin amfani da su ta hanyar da bata dace ba, kana su kasance masu bin tsari da kuma dakokin addinan da suke bi wadanda suke da koyar da tarbiya.

Kazalika, dantakarar kujerar majalisar dattawan Najeriya a mazabar jihar Taraba ta kudu dake yankin Arewa maso gabashin kasar ya bayyana cewa muddun ya kai ga gaci zai mayar da hankali inganta fannin ilimi da bunkasa rayuwar matasa domin sune ginshikin ci gaban kowace al’umma.

Mr Jimkuta ya ce yana da yakinin cewa jam’iyyar APC zata kai ga gaci a jihar Taraba yayin babban zaben dake tafe a Najeriya.

 

Ak

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *