Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben 2023: Kungiyar ANA Ta Bayyana Goyan Bayanta Ga Tinubu

Musa Aminu, Abuja

0 171

Kungiyar dake fafufutukar sake inganta rayuwar al’umar Arewacin Najeriya wato AREWA NEW AGENDA ko kuma ANA a takaice, ta bukaci al’umar kasar da su sanya dukkanin yan takarar shugabancin Najeriya a sikeli domin la’akari da rawar da suka taka a mukaman da suka rike a baya kafin su yanke shawarar wanda zasu zaba yayin babban zaben dake tafe.

Shugaban kungiyar Sanata Abubakar Ahmad Mo’alliyidi shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da suka gudanarranar juma’a a Abuja fadar mulkin Najeriya.

Taron mai taken a gani a kasa ba labari ba, ya kunshi yin amfani da kafafan yada labarai domin bayyana hotunan ayyukan da dantakarar shugabanci Najeriya a inuwar jam’iyyar APC Bola Amhed Tinu ya aiwatar a lokacin da yake gwamnan jihar Legas dake kudu maso yammacin kasar, a cewar shugaban kungiyar ta Arewa New Agenda ko kuma ANA dake fafutukar inganta rayuwar al’umar Arewacin Najeriya, Sanata Abubakar Amhad Mo’alliyidi sai da suka gudanar da bincike mai zurfi kafin su yanke shawarar goyon bayan tsohon gwamnan jihar ta Legas duba da ayyukan raya kasa da kuma dumbin al’umma da ya raina wadanda da dama daga cikinsu yau ake alfahari da su a kasa.

A nashi bangaren, Jigo a kungiyar ta ANA Hon Sa’idu Boboi ya ce kungiyar na da wakilcin kowane kabila daga daukacin jihohin Arewacin  Najeriya 19 da kuma manyan addinan kasar, kana manyan manufofin da suka sanya a gaba su ne ci gaban yankin da suka fito dama kasar baki daya.

kazalika, shugaban kungiyar ta AREWA NEW AGENDA ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa muddun Bola Ahmed Tinubu da mataimakisan Sanata Kashim Shatima suka kai ga gaci za su ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya assasa

Taron dai ya gudana ne a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja babban birnin Najeriya a daidai lokacin da ya rage mako guda a gudanar da babban zaben kasar.

 

AK

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *