Hukumar Kula da kadarori ta Najeriya (NCP) a karkashin jagorancin mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ta amince da kamfanoni tara da su gaggauta aiwatar da tantancewar Kanfanin Gidan waya NIPOST a fadin kasar .
Kamfanonin da suka kasu zuwa shiyyoyi shida na siyasar kasar nan sune, Oghogho Ayanru, Raji Adewale Associates, Alaba Odunlanmi, Law Field Barristers da lauyoyi da B.A. Wali & Associates, sauran su ne, Aliyu Abubakar & Co, Bola Fabola, Tayo Osuntogun & Co da Primal Chambers.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen hulda da jama’a na Ibeh, Uzoma Chidi ta bayyana cewa wannan na daya daga cikin muhimman batutuwa a taron majalisar karo na 2 na shekarar 2023.
After deliberation, the Council approved the appointment of Mainstream Energy Solutions as the preferred bidder in the concession of the Zungeru HydroElectric Power Plant. pic.twitter.com/avcKJij5Cb
— Prof Yemi Osinbajo (@ProfOsinbajo) February 23, 2023
Sanarwar ta ce: “Kamfanonin za su ba da shawarwari don gudanar da aikin bisa ga Tabbatar da sunayen kadarorin, ta yadda za a tantance ko an yi rajistar kadarorin a cikin rajistar filayen da suka dace, da tantance matsayin mallakar kadarorin da kuma nau’in, girman, da wuri na kaddarorin; da kuma ba da duk wani ƙarin bayani da zai inganta binciken kadarorin.”
Leave a Reply