Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Najeriya Ya Taya Sabon Shugaban G24 Murna

Aisha Yahaya, Lagos

0 162

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya sabon Darakta kuma shugaban sakatariyar kungiyar gwamnatocin kasashe ashirin da hudu G24, Dakta Iyabo Masha na Najeriya murna.

 

 

A wata wasika da ya sanyawa hannu, shugaba Buhari ya bayyana cewa, ta wannan nadin, Dr. Masha ya kafa tarihi, inda ya zama dan Afrika na farko da ya taba rike mukamin tun bayan kafa kungiyar a shekarar 1971.

 

 

Shugaban ya bukaci Dr. Masha da ya yi amfani da wannan matsayi wajen jajircewa wajen samar da ci gaban kasashe masu tasowa, musamman kan muhimman kalubalen tattalin arziki da suka hada da sauye-sauyen tattalin arziki, warware basussuka, manufofin haraji da bunkasa fannin hada-hadar kudi.

 

 

“Bayan yin aiki kafada da kafada da Dokta Masha a lokacin da ta yi aiki tare da majalisar ba da shawara kan tattalin arziki na shugaban kasa, ba ni da wata shakka a raina cewa tana da himma, sadaukar da kai ga aiki, da ƙwararru ma’aikata.

 

 

“Ina taya ku murna, Najeriya na alfahari da nasarar da kuka samu, kuma ina yi muku fatan alheri,” in ji shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *