Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasar Sudan ta Kudu ya kori ministan harkokin wajen Shi

Aisha Yahaya, Lagos

0 231

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya kori ministan harkokin wajen shi. Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda da korar ministocin tsaro da na cikin gida.

 

 

Rahoton ya ce babu wani bayani da aka bayar kan korar Mayik Ayii Deng, wanda aka sanar a cikin wata sanarwa.

 

 

Ministan da aka kora dai abokin Mista Kiir ne kuma ya taba rike mukamin minista a ofishin shugaban kasar.

 

 

A halin da ake ciki, korar da aka yi a makon da ya gabata ta yi barazanar kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da madugun ‘yan adawar mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar.

 

 

‘Yan adawar dai sun bukaci a mayar da Angelina Teny bakin aiki, wadda Mr. Kiir ya kora daga mukamin ministar tsaro tare da mika wa jam’iyyarsa mukamin.

 

 

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin da su “dau matakin kamun kai tare da shiga cikin ruhin jami’a domin warware irin wadannan batutuwan kasa da kasa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *