Dantakarar gwamna na Jam’iyyar PDP a jihar Katsina ya jaddada takarar sa ta neman gwamnan jihar
Kamilu Lawal,Katsina.
Dan takarar gwamnan jihar Katsina dake arewa maso yammacin najeriya kalkashin jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana cewa yana nan kan takararsa ta neman gwamnan jihar Katsina a zaben ranar 18 ga watan Maris mai zuwa kamar yadda hukumar zaben kasar INEC ta shirya.
Dantakarar ta bakin babban darektan yakin neman zaben sa, Dakta Mustapha Inuwa wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Katsina, yace labarin da ake yadawa na cewa dantakarar, sanata Yakubu Lado ya janye takarar sa babu kamshin gaskiya a cikin sa.
“Ina tabbatar ma al’ummar jihar Katsina, musamman magoya bayan jam’iyyar PDP cewa Sanata Yakubu Lado Danmarke yana nan a matsayinsa na dantakarar gwamnan mu, sabanin yadda wasu ke rubuta takardun karya ana ta yadawa cewa ya janye takararsa,
“Al’ummar jihar Katsina su sani cewa Yakubu Lado da mataimakin sa arch.Aminu Yar’adua suna nan a matsayin yantakarar gwamna kuma muna rokon su su fito su kada masu kuri’a a ranar Asabar 18 ga watan Maris din nan da su da yantakarar majalisun dokoki kalkashin jam’iyyar PDP”, inji Mustapha Inuwa.
Ya kara godema al’ummar jihar bisa yadda suke nuna tarayyar su da jam’iyyar PDP a jihar tare da kira garesu da su sake fitowa a ranar Asabar 18 mai zuwa domin kada ma jam’iyyar PDP kuri’unsu domin samun nasarar yantakarar ta a fadin jihar.
“Muna da tabbacin cewa madamar za’a aje akwati a mazabu to jam’iyyar PDP ce zata samu nasara a fadin jihar nan”, inji shi.
Babban darektan yakin neman zaben ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar su gudanar da harkokin su cikin lumana a ranar zaben, yana mai bada tabbacin kwamitin zaben na jagorantar magoya bayan jam’iyyar gudanar da zaben cikin zaman lafiya da lumana.
“Yana mai cewa mun san jama’ar jihar Katsina suna tare da PDP kuma zasu kauracema duk wani shiri na kokarin a tunzura su su biyema shirin tayar da hankalin al’umma a lokacin zaben da kowa ya san jam’iyyar mu ce ke da nasara”.
Leave a Reply