Dan takarar gwamna na jam’iyyar Young Progressive Party YPP a jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya, Dr Sunday Opoke ya musanta rugujewar tsarin siyasar sa bisa zarginsa da goyon bayan dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
Dr Opoke ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abakaliki babban birnin jihar.
Ya ce ba zai taba ruguza burinsa na zama Gwamnan Jihar ba don kawai ya goyi bayan wani dan takara.
“Ni, Dokta Sunday Opoke, dan takarar gwamna na jam’iyyar YPP ta Youth Progressive Party a jihar Ebonyi, ban janye wa wata jam’iyyar siyasa ba, kuma ba zan taba yin irin wannan abu ba. Idan wani ya yi zargin cewa na sauka ne domin in goyi bayan dan takarar Gwamna a APC, to irin wannan mutumin ya fito da shaidarsa.”
“Na yi wannan zaben ne domin in yi nasara domin ‘yantar da jama’ar jihar da kuma samar da rayuwa mai kyau ta kowane fanni”
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin kada masa kuri’a a zaben gwamna mai zuwa domin samar da zaman lafiya mai dorewa a dukkan sassan jihar.
“Gwamnatinmu za ta kawo saukin harkokin kasuwanci a jihar. Haka kuma za ta kawo karshen duk wani rikicin kabilanci da ke faruwa a jihar”
“Dukkan mutanen Ebonyi za su sami damar samun ababen more rayuwa idan aka zabe ni kan mulki,” in ji Opoke.
Dan takarar Gwamnan ya ce zai yi maraba da dukkan jam’iyyun siyasar jihar bayan lashe zabe a karkashin jam’iyyar YPP domin su taimaka wajen musayar ra’ayoyin da za su kara daukaka martabar jihar.
Leave a Reply