Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Muryar Najeriya VON Ya Bukaci A Kaddamar Da Shugabancin Majalisar Dattawa Na 10 Zuwa Kudu Maso Gabas

Aliyu Bello Mohammed

0 197

Shugaban Muryar Najeriya (VON), Mista Osita Okechukwu, ya bukaci a Bada shugabancin majalisar dattawa karo na 10 a wannan karon ya koma yankin Kudu maso Gabas domin kiyaye gaskiya da adalci.

 

 

Okechukwu, wanda shi ne wanda ya kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

 

 

“Najeriya na kan tafiya tukuru kuma tunda Kudu-maso-gabas ba ta samu shugaban kasa ko mataimaki ba, ya kamata a fara tunanin dabarar fara aiwatar da sulhu da farfado da yankin.

 

 

“Eh, na yarda Kudu-maso-Gabas ba su zabi babbar jam’iyyata ba; duk da haka, dole ne shugaban ya yi tunanin yadda rayuwa Zata kasance nan gaba.

 

 

“Yankin ya samu ƙwararrun Sanatoci waɗanda za a iya zaɓar wani daga ciki ya samu mukamin Shugaban Majalisar Dattawa.

 

 

“Abin farin ciki, muna da zababbun ‘yan majalisar dattawa guda shida: biyu daga cikinsu suna kan gaba – Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Osita Izunaso. Mu zabi daya daga cikinsu.

 

 

“Ko kadan babu wanda zai zarge mu saboda ba mu da wani Sanata, wanda hakan ya faru a shekarar 2015.

 

 

“Mu ‘ya’yan gidauniyar APC muna bukatar ‘yan’uwanmu maza da mata a wasu yankuna na siyasa.

 

 

“A kan manyan Sanatoci guda biyu da ke gaba, daya zai fi son Orji Uzor, wanda shi ne wanda Zai cike guraben Kudu maso Gabas.

 

 

“Dan uwana Izunaso yana da kwarewa akan dimokaradiyya , amma shi kuwa Orji ne nasa.

 

 

“Orji ya yi karatu a arewa, yana kasuwanci a Legas kuma ya fi Pan-Nigeria,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *