Jami’an tsaro sun cafke wasu mutane da dama a karamar hukumar Isi-Uzo da ke jihar Enugu inda suka haifar da tashin hankali da fargaba a tsakanin mutanen da suka taru a rumfunan zabe na zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan sandan jabu ne sun mamaye karamar hukumar domin kawo cikas a zaben yayin da rundunar hadin gwiwa ta sojoji da ‘yan sanda da Civil Defence suka cafke wasu masu laifin.
An tabbatar da ci gaban a safiyar ranar Asabar ta hannun Bishop na Anglican na Eha-Amufu Diocese, Rt. Rev. Daniel Olinya.
Bishop din ya shaidawa manema labarai cewa “Hukumomin tsaro na karya sun yiwa Isi-Uzo kawanya.”
Ya bayyana cewa a rumfar zabe da ya kamata ya kada kuri’a lamarin bai bambanta ba. “Lokacin da na isa rumfar zabe ta a Umuokpara, ‘yan wata jam’iyyar siyasa suna tsoratar da masu kada kuri’a wadanda suke ganin ba sa goyon bayan jam’iyyarsu. Da na yi magana, sai suka daka min tsawa.
“Na yi tambaya game da kasancewar ‘yan sanda da wata mata sanye da silifas. Lokacin da na tambayi katin shaidarta, sai ta nuna min hula.
“Wannan shi ne halin da ake ciki a dukkan rumfunan zabe a Eha-Amufu…Muna kira ga kwamishinan ‘yan sanda da ya yi wani abu game da wannan mummunan yanayi,” in ji Bishop Olinya.
Leave a Reply