Take a fresh look at your lifestyle.

Zaben Gwamna Na Sokoto: Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Ya Kada Kuri’a Ya Yaba Da Tsarin

0 338

Ministan harkokin ‘yan sandan Najeriya Muhammed Dingyadi ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan shirye-shiryen da aka yi na zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.

Ministan ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ya kada kuri’arsa a mazabar sa ta Dingyadi mai lamba 003 da safiyar yau.

Ya ce, kalubalen da aka fuskanta a zabukan shugaban kasa kamar tashe-tashen hankula daga ‘yan bangar siyasa, rashin zuwan kayan zabe da sauran su an magance su a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha.

Dingyadi ya yabawa alkalan zaben bisa aikewa da kayan zabe rumfunan zabe akan lokaci. Ya kuma yaba da ingantuwar tsaro a rumfunan zabe, lamarin da ya taimaka wajen magance tashe-tashen hankulan zabe.

Ministan harkokin ‘yan sandan ya kuma yabawa dimbin fitowar masu kada kuri’a a jihar Sokoto da kuma yadda suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *