Take a fresh look at your lifestyle.

Ahmad Aliyu na APC Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Sokoto

Aisha Yahaya, Lagos

0 195

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmad Aliyu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto

 

 

Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’in kula da masu kada kuri’a na jihar Sokoto, Farfesa Armiya’u Hamisu, ya ce “An bayyana Aliyu ne a matsayin wanda ya lashe zaben kuma aka dawo da shi bayan ya samu kuri’u 45,3661.”

 

 

 

Sai kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Malam Sai’du Umar, wanda ya samu kuri’u 40,4632. Aliyu ya lashe kananan hukumomi 19 cikin 23 an jihar yayin da Umar na PDP ya lashe kananan hukumomi hudu a zaben ranar 18 ga watan Maris

 

 

Farfesa Hamisu shi ne mataimakin shugaban jami’ar tarayya dake Dutse a jihar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *