Afirka ta Kudu tana sane da wajibcinta na shari’a, in ji mai magana da yawun shugaban kasar Cyril Ramaphosa yayin da yake magana kan ziyarar da Vladimir Putin ke shirin kaiwa bayan wata kotun duniya ta bayar da sammacin kama shugaban na Rasha.
A watan Agusta ne ake sa ran shugaban kasar Rasha Putin zai ziyarci kasar Afirka ta Kudu domin halartar taron kasashen BRICS. “Mu a matsayinmu na gwamnati muna sane da hakkinmu na doka.
Koyaya, daga yanzu zuwa taron kolin za mu ci gaba da kasancewa tare da masu ruwa da tsaki daban-daban, ”in ji mai magana da yawun Vincent Magwenya.
Duk da yake babu wani tabbaci a hukumance kan ziyarar ta Putin, ana sa ran zai halarci taron BRICS karo na 15, kamar yadda ya yi a shekarar 2013.
Sai dai irin wannan ziyarar za ta sanya gwamnatin Ramaphosa, wadda ba ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ba, a cikin wani mawuyacin hali bayan sammacin kama shi da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta yi.
“Ya kasance alƙawarin Afirka ta Kudu da matuƙar sha’awar ganin an warware rikicin Ukraine cikin lumana ta hanyar tattaunawa.”
Comments are closed.