Take a fresh look at your lifestyle.

APC Za Ta Samar Da Tsaro A Jihar Sokoto : Ahmed Aliyu

Shehu Salman, Sokoto

0 198

Zaɓaɓɓen gwamna a jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya Alhaji Ahmed Aliyu Sokoto ya sha alwashin cika dukkanin alƙawullan da ya ɗaukar wa al’ummar jihar a lokacin da ya ke zawarcin ƙuri’unsu, alƙawullan da suke ƙunshe cikin wani ƙudurorinsa guda tara da ya yi wa laƙabi da 9 point agenda waɗanda suka haɗa da ilimi da yaƙi da talauci da samar da tsaro da kiwon lafiya da kare muhalli da dai sauransu.

Jam’iyar adawa ta APC a jihar Sokoto kuma mai mulki a Najeriya ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris ɗin nan da kuri’u 453,661 inda ya done abokan hamayyarsa sama da shida da suka kara tare.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya zargi gwamnantin PDP da gazawa wajen gudanar da ayyukan ci gaba ga al’ummar Sokoto tsawon shekaru kusan Takashi.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *