Tsohon gwamnan jihar Osun, Isiaka Oyetola, ya taya ‘yan uwa musulmi na jihar da ma duniya baki daya murnar ganin watan azumin Ramadan.
Oyetola ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan wata mai alfarma don karfafa imaninsu, da neman kusanci ga Allah da samun “taqwa” (taqwa) wanda ya ce, shi ne babban abin da ake bukata na azumin wannan wata na Ramadan.
Ya kuma bayyana watan Ramadan a matsayin wata mai tarin albarka da rahama da gafara daga Allah, sannan ya bukaci al’ummar Musulmin jihar Osun da su yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa addu’o’in ci gaba da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Ya kuma yi kira ga musulmi da wadanda ba musulmi ba da su nuna soyayya, hakuri da juna, tausayi da zaman lafiya a cikin wannan wata da ma bayansa.
“Ina taya ‘yan uwa Musulmi mazauna jihar Osun da ma duniya baki daya murnar shigowar wata mai alfarma na Ramadan. Yayin da muka fara wannan wata, ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba mu lafiya da karfin gwuiwa wajen gudanar da azumi da sauran ibadu.
“Mu kuma mu yi amfani da wannan lokacin wajen karfafa addu’o’i ga kanmu, jiharmu da kasarmu. Ina rokon Allah Ya karbi dukkan ayyukanmu na Ibaadah, Ya biya mana bukatun zuciyarmu. Ya ci gaba da ba mu rahamarSa, ƙauna, shiriya da kariyarsa marar iyaka. Ramadan Kareem gare ku da masoyanku,” in ji Oyetola.
Leave a Reply