Take a fresh look at your lifestyle.

Zababben Shugaban Kasa Ya Yi Kira Ga Musulmai Da Suyi Wa Bil Adama Hidima

0 137

Zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmin Najeriya a yayin da suke fara azumin watan Ramadan, da su yi koyi da tawali’u, gafara da kuma hidimtawa wasu.

 

 

Tinubu, ya shawarci al’ummar Musulmi da su yi addu’a domin hadin kan al’umma tare da gudanar da rayuwarsu ta yadda zai samar da kasa mai inganci ga kowa.

 

 

Ya kuma bukace su da su yi wa shugabannin Najeriya addu’a a wannan lokaci na azumi da addu’o’i.

 

 

“Yayin da muke cikin azumi da tunani na ruhi, mu ci gaba, cike da ruhin sadaukarwa, horo, son rai, adalci, hakuri, jinkai, tausayi da karamcin da ke cikin zuciyar Musulunci.

 

 

“Mu yi kokari mu yi koyi da Annabi Muhammad (SAW) na tawali’u, gafara, da hidima ga wasu.

 

 

“Mu ci gaba da tafiya ta wannan hanya domin mu mai da kanmu al’umma nagari da al’umma da dukkan mutane musulmi da wadanda ba musulmi ba za su rayu cikin aminci da zaman lafiya da adalci kamar yadda Allah Ya so.

 

 

“Yayin da muke yin addu’a ga Allah, mu kuma tuna kasarmu da shugabanninmu a cikin addu’o’inmu.

 

 

“Bari mu tuna bambancin mu don manufa ne kuma muyi addu’a cewa dukkanmu mu yi aiki don ƙarfafa shi. Dole ne mu hada hannu don kawo ci gaba a Najeriya ta hanyar yin addu’ar hadin kai da ci gaba. Darussan watan Ramadan na nuni ne ga nasarar hadin kai, ba gazawar rarrabuwa ba.” Inji Tinubu.

 

 

Ku tuna cewa a ranar Talata 21 ga watan Maris ne Mista Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasashen Turai domin hutawa, da gudanar da aikin hajji da kuma tsara shirin mika mulki gabanin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

 

 

Zai huta a Paris da Landan sannan zai wuce Saudiyya don yin Umrah da Azumin Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *