Take a fresh look at your lifestyle.

Ba hannun mu a neman sake zaben gwamna a Kano – SOs

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

27

Gamayyar kungiyoyin sakai (CSOs ) da suka sa ido kan zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jiha da aka yi ranar 18 ga watan nan na Maris sun nesanta kansu da neman a sake zaben da aka yi a na gwamna a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya.

 

 

Kungiyoyin na Transition Monitoring Group (TMG) da Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) da Kano State Civil Society Elections Situation Room (KSCSESR) sun kira taron manema a wannan Asabar inda suka barrannata kansu da rahotanni da suke neman a sake zaben gwamna a Kano wanda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi.

 

 

A cewar gamayyar kungiyoyin akwai wata kungiya da ake zargin na da alaka da ‘yansiyasa  wacce ke yada labaran karya da sunan kungiyoyin sakai na hakika.

 

 

Jagoran masu sa idanun na TMG kuma shugaban kungiyar CISLAC Comrade Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani da yake bayani ga manema labarai a Kano yace “Babu wata kungiya ta hakika da za ta raba kanta da wata jam’iyyar siyasa, domin waccan kungiya da ke ikirari da sunan ‘yar fafutuka ta dauki wani bangare na siyasa.”

 

 

A cewar Rafsanjani dai wadanda suka yada rahotannin karya karkashin wata kungiya mai suna Accredited INEC Elections Observers “Kungiya ce ta bogi da ba a san da ita ba, wacce ‘yansiyasa ke daukar nauyi.”

 

 

Da yake nasa tsokaci  jagoran kungiyar Kano Civil Society Elections Situation Room, Ambasada Ibrahim Waiya, ya ja hankalin kafafan yada labarai su rika banbance sahihan kungiyoyin sakai da wadanda ‘yansiyasa ke daukar nauyinsu wadanda ke fakewa karkashin kungiyoyi sanannu don cimma bukatar kansu ta son rai.

Comments are closed.