Take a fresh look at your lifestyle.

Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Ya Nemi Ci Gaba Da Hulda Da Katar

0 238

Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika ya jaddada bukatar Najeriya da Qatar su ci gaba da kulla alaka mai dorewa, inda ya bayyana cewa Najeriya na sha’awar zuba jari, kuma ta kuduri aniyar aiwatar da manufofinta na saukin kasuwanci ga masu zuba jari.

 

 

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban ‘yan jaridu da hulda da jama’a na ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya, Mista Odutayo Oluseyi a Abuja babban birnin kasar.

 

 

Sirika ya ce adadin kudaden da ake samu wajen zuba jari a Najeriya ya kai kashi 34% kuma mafi girma a duniya, mai yawan al’umma sama da miliyan 200, ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da mai kula da harkokin kasar Qatar, Mista Ahmed. Mohammed Al-Hor ga Ministan Abuja.

 

 

A cewar Ministan, Qatar kasa ce mai samar da mai tare da sauran fannonin zuba jari kamar Najeriya wacce take da kayayyakin more rayuwa da ake bukata domin gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki.

 

 

Sirika ya ci gaba da cewa, akwai bukatar Najeriya da Qatar su inganta manufofinsu na biza duba da cewa, takunkumin da aka yi wa bangarorin biyu na yin wahalar cudanya tsakanin kasashen biyu kamar yadda ake tsammani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *