Jam’iyyar Peoples Democratic Party, ta kafa kwamitocin zabe na mazabar Ward Congress, domin gudanar da taron gundumomin jam’iyyar a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi, da nufin zabar wakilan kananan hukumomi uku a jihohin.
Jam’iyyar a wata sanarwa ta daban ta hannun sakataren kungiyar ta kasa Umar Bature a Abuja ranar Talata, ta bayyana cewa kwamitin ayyuka na jam’iyyar NWC ne ya amince da nadin.
Bature ya ce an shirya gudanar da taron ne a ranakun Talata da Laraba a kowace unguwanni 105 da ke Bayelsa, 305 a Imo da 234 a Kogi.
A cewar Bature, Sanata Bukola Saraki ne ke jagorantar kwamitin na Bayelsa, Abdul Ningi na Kogi da Henri Terebe na jihar Imo.
Comments are closed.