Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rantsara da Tsohon Supeta Janar na ‘yan sandan kasa, Solomon Arase, a matsayin Shugaban Hukumara ‘yan sanda.
An gudanar da bukin rantsarwar a Fadar Shugaban Kasa dake, Abuja, jim kadan kafain fara taron Majalisar Zartaswa.
Arase ya karbi ragamar mulki daga Musliu Smith, wanda kuma tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda ne.
Tsohon Shugaban Hukumar, Musiliu Smith, ya yi murabus a watan Satumba, 2022 bayan haka wata mamba a hukumar mai shari’a Clara Ogunbiyi mai ritaya ta koma matsayin shugaban riko na Hukumar.
Shugaban ya kuma rantsar da mambobin kwamitin da’ar ma’aikata biyar.
Su ne Murtala Kankia daga jihar Katsina, don wakiltar yankin Arewa maso Yamma; Zephaniah Bulus daga jihar Nasarawa, mai wakiltar Arewa ta tsakiya da Farouq Umar daga jihar Yobe mai wakiltar Arewa maso Gabas.
Sauran sun hada da Abdulsalam Olawale daga jihar Ondo mai wakiltar Kudu maso Yamma da kuma Farfesa Juwayriya Badamasiuy daga jihar Kogi mai wakiltar Arewa ta tsakiya.
Majalisar ta kuma yi shiru na minti daya domin karrama tsohon hafsan hafsoshin tsaron kasar, Janar Oladipo Diya.
Diya, Laftanar Janar mai ritaya, wanda ya taba rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha, ya rasu ne a ranar Lahadi 26 ga Maris, 2023 yana da shekaru 79 a duniya.
Ya kuma kasance Gwamnan Soja na Jihar Ogun daga Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.
A halin da ake ciki, shugaba Buhari ne ke jagorantar taron majalisar a zauren majalisar dokokin jihar.
Comments are closed.