Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Jarabawa ta Kasa Ta Tsawaita Lokacin Rijistar SSCE 2022

0 426
Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO) ta kara wa’adin rijistar jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2022 (SSCE), ga ‘yan takarar da suka shiga makaranta, zuwa tsakar daren Litinin 20 ga watan Yuni, 2022.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai, ta hannun babban mai kula da kafafen yada labarai na majalisar, Azeez Sani.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa tun da farko an shirya rufe wa’adin rajista a ranar Litinin, 30 ga Mayu, 2022.

Sannan ya bayyana cewa Ma’aikatun Ilimi na Jihohi, Shugabanni, da duk masu ruwa da tsaki su lura cewa ba za a sake yin wani kari ba.

Jarrabawar shaidar kammala sakandare ta NECO ta shekarar 2022 (SSCE) za ta fara ne a ranar 27 ga Yuni, 2022 kuma za ta kare ranar Juma'a 12 ga Agusta, 2022.

Za a yi wa ’yan takara gwaji ne a darussa 76 yayin jarrabawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *