Wata Tawagar Taimakawa Fasaha Ta Bankin Duniya Karkashin Jagorancin Task Team on Multi Sectoral Crisis Recovery Project (MCRP) Serena Cavicchi, ta ziyarci jihar Borno kan tantance ayyuka, lura da wasu ayyuka da aka zaba da kuma taimakawa wajen inganta ayyukan kungiyar MCRP a jihar Borno.
Sauran membobin tawagar Taimakon Fasaha sun hada da mai ba da shawara ga Bankin Duniya kan aikin MCRP Mista Masroor Ahmed, Chidozie AG, Masanin Tattalin Arziki na Noma, Anas Abba Kyari, Babban Jami'in Harkokin Kasuwanci, Farfesa Ahmed Chinade Tsaron Muhalli da Nkem Uzochukun C1 da C3 kwararre.
Bayan wani zama na musamman da gwamnatin jihar Borno jami'an MCRP suka yi a dakin taro na Technology Incubation Hub dake Maiduguri tawagar karkashin jagorancin kodinetan MCRP na jihar Borno Baba Zanna Abdulkarim sun ziyarci daya daga cikin cibiyoyin lafiya 25 da wannan aikin ya gina a unguwar talakawan Abujan. Jami’in kula da asibitin Yachilla Waziri ya ce bayan gina cibiyar kiwon lafiya a matakin farko, aikin ya kuma tallafa wa silinkin da hasken rana da rijiyoyin burtsatse da muhimman magunguna.
Leave a Reply