Zaben Fidda Gwani na APC: Shugaban Jam’iyyar Na Kasa Ya Bukaci Hadin Kai Gabanin Zaben 2023
Abdulkarim Rabiu
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga yayan jamiyyar da su hada kai da sahihancin manufa domin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.
Sanata Adamu ya yi kiran ne a jawabinsa na maraba a babban taron jam’iyyar APC na musamman na zaben dan takararta na shugaban kasa a babban zaben Najeriya na 2023.
Ya bayyana cewa ”Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa da aka zaba kuma ya fara aiki a watan Maris na wannan shekara ya yi kokarin hada kan ‘ya’yan jam’iyyar tare da sulhuntawa tun lokacin da ya fara aiki.”
Shugaban jam’iyyar APC-n na kasa ya ce “ana iya ganin shaidar hadin kai a zaben fidda gwanin da aka fi samun nasara wanda aka gudanar a dukkan jihohin kasar. ”
Sanata Adamu ya yabawa ‘yan takarar shugaban kasa da suka janye daga takarar.
Ya Kara da cewa jita-jita da karairayi sun mamaye kafafen yada labarai game da taron fidda dantakar shugaban kasa na jam’iyyar APC, sannan ya yi kira ga ‘yan siyasa da sauran al’umma da kada su yi amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki wajen tauye hakkin jama’a.
Da yake magana game da zaben shugaban kasa, ya shawarci Wakilai masu zabe wato “delegates da kada su kada kuri’a saboda domin son rai amma su zabi dan takarar da zai nuna cikakken kudurin APC ga Najeriya. ”
Ya kara da cewa wajini ne Wanda aka zaba da ya ci gaba da aiwatar muradan shugaban kasa Muhammadu Buhari na samar da sabuwar Najeriya.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply