Masu ruwa da tsaki a harkar kasa da kasa sunyi kira ga kasar Slovakia da ta mara wa Najeriya a bangaren ci gaban binciken tsarin Demokuradiya.
Shugaban Cibiyar harkokin kasa da kasa, Farfesa Eghosa Osaghae shine yayi wannan kira wajen taron jakadu da aka gudanar a Legas mai taken hulda tsakanin Najeriya da Slovakia.
Daraktan yace Najeriya ta sadaukar da kanta akan ci gaba da kyakyawar alaka da sauran kasashe musamman a manufofin harkokin waje da take ganin tana da alaka da Slovakia.
A nasa jawabin jakadan Slovakia a Najeriya, Mr Thomas Felix cewa yayi tun lokacin da Najeriya da Slovakia suka samu ‘yancin kasa suka kulla huladar arziki a 1st Janairu,1993 .
Mr. Felix yace Slovakia ta goyi bayan Najeriya a yakin da take akan ‘yan taadda,Bunkasa tattalin arziki da aiyyukan Noma.
Professor Osaghae ya kuma ce Najeriya nada burin bunkasa tsarin Demokuradiyara ta mai dorewa.
Ya tunatar da cewa Najeriya nada burin tabbatar tsarin wazar da zaman lafiya a duniya baki daya.
Ladan Nasidi
Leave a Reply