Take a fresh look at your lifestyle.

Sada Soli Ya Bayyana Ra’ayinsa Na Takarar Kakakin Majalisar Wakilai

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 298

Dan Majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Mazabar Jibya da Kaita a jihar Katsina ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takarar kakakin Majalisar Wakilai ta goma da zata fara aiki daga ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Hon. Sada Soli ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da Muryar Najeriya a ofishinsa dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce kasancewarsa ya jima a Majalisar yana kuma da kwarerewa sosai, inda a cewarsa tun a shekara ta 1992 yake Majalisar, a don haka yana da abin da zai yi ya takaimaki al’umma da ita Kanta Majalisar idan ya zama kakakin Majalisar wakilai.
A cewarsa ya san duk abubawan dake faruwa a cikin Majalisar, in da aka yi kurakurai da inda aka yi daidai da Kuma wuraren da ake bukatar gyarawa.
” Wannan damar da Allah ya bani na zauna a cikin Majalisar tun 1992 , an yi kakakin Majalisar har sai sau tara a gabana na sansan kurakuran da aka yi , na san abubuwan da aka yi na dai dai saboda haka idan akwai tunanin ganin inda mutun zai taimaka ya ga an ci gaba da gudanar da abubuwa na daidai da wadandan akai yi kurarakurai a gyara domin al’umma ta samu inganci da ita Kanta Majalisar ta samu hanyar inganta tafiyar da al’amuranta. Duk wadannan dalilai su suka bani tunanin mai zai hana in yi amfani da damar da nake da ita domin muga yadda za mu taimaki Najeriya” In ji Sada Soli

Hon. Soli ya kara da cewa idan Allah ya bashi nasara ya zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya zai maida hankali akan akan tsare mutuncin yan Najeriya.

Ya ci gaba da cewa ” Za mu maida hankali akan yin dokokin da za su tsare mutuncin kasa a ciki da wajenta, za mu maida Wajen hada karfi da karfe da duk wadanda da ke cikin Majalisar imma dan Jam’iyya mai rinjaye ko Kuma mara rinjaye domn Samar da mafita wanda Najeriya za ta ci gaba”.

Sada Soli ya ce zai tabbatar da hadin Kai tsakanin Majalisar da bangaren zartarwa da gwamnatin jihohi da kuma kananan hukumomi.
“Duk wanda ya Kawo al’amarinshi a Majalisa za mu zauna da idon basira mu kalleshi domin a yi wa kasa aiki, al’umma ta ci gaba”

Dangane da batun karba karba kuwa, Sada Soli ya ce la’akari da cewa Shugaban kasa ya fito daga kudu maso yamma, maitamikin Shugaban kasa Kuma daga arewa masu gabas, yankin arewa maso yamma shi ya fi cancanta a baiwa kujerar Kakakin Majalisar Wakilai duba da dunbun kuri’u da ya ke samarwa a duk lokacin da aka yi babban zabe a Najeriya.

Abdulkarim Rabiu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *