EU, Amurka Suna Sa-ido Kan Aiwatar Da Zaman Lafiya A Yankin Tigray A Habasha
Jami’in kula da harkokin waje na EU ya ce EU da Amurka suna sa ido kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a Habasha kuma sannu a hankali za su maido da dangantakarsu da Addis Ababa.
“Da farko, a Habasha, wannan babban rikici ne kuma yanzu, abin farin ciki, abubuwa sun fara tafiya don magance shi. Wannan ɗaya ne daga cikin manyan labarai masu daɗi da muke da su a duniya. Kuma don dorewar ci gaban da ake samu a yanzu, dole ne EU da Amurka su ci gaba da aiki kafada da kafada.” Josep Borrell, EU ya ce “Sakon zuwa ga gwamnatin Habasha da na Tigrayan biyu shi ne mu fahimtar da su cewa muna kallon yadda za a sasanta rikicin kuma za mu daidaita dangantakarmu a hankali a hankali, mataki-mataki”, in ji Josep Borrell, EU. Shugaban Siyasar Harkokin Waje.
Yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya hannu a ranar 2 ga Nuwamba, 2022 a Pretoria ta kawo karshen kazamin rikici na tsawon shekaru biyu a yankin Tigray da ke arewacin Habasha tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da kuma ‘yan tawayen kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF).
Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 500,000 a cewar Amurka.
Aisha Yahaya
Leave a Reply