A ranar Laraba ne Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta karrama marigayi tsohon Alkalin Kotun Duniya, Yarima Bola Ajibola, wanda ya rasu a ranar Asabar, 8 ga Afrilu, 2023, yana da shekaru 89 a duniya.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da rasuwar Ajibola a hukumance kafin a fara taron majalisar wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta tare da yin shiru na minti daya domin karrama shi.
Bayan sanarwar, Majalisar ta yi shiru na minti daya don girmama marigayi masanin shari’a wanda ya kasance a Kotun Duniya da ke Hague, Netherlands, daga 1991 zuwa 1994.
Kafin lokacin, Alkali Ajibola ya kasance babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’a a zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida (Rtd) daga 1985 zuwa 1991.
Ya kuma kasance shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, daga 1984 zuwa 1985.
An binne gawar marigayi Alkali Ajibola a ranar Lahadi a Abeokuta, jihar Ogun.
Leave a Reply