Take a fresh look at your lifestyle.

2023: Babbar Jam’iyyar Adawa ta Najeriya Ta Zabi Dan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

By Paul Oke, Abuja

0 208

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta, Dr Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne a sakatariyar  jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Aitiku Abubakar ya ce ya yanke shawara akan Dr Okowa ne saboda yana da kwarewar da zai iya kasancewa mataimakin shugaban kasa.

Dan takarar shugaban kasar ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da suka hada da Gwamnoni, kwamitin ayyuka na kasa, kwamitin amintattu, da sauran shugabanni domin neman shawararsu.

 

AK/LADAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *