Take a fresh look at your lifestyle.

Cibiyoyin Nijeriya Za Su Haɗa Kan Ma’aikatan Horar Da Ma’aikata

0 253

Cibiyar Horas Da Sojoji Ta Najeriya, NDA ta gabatar da wata shawara ga masu yi wa kasa hidima, NYSC kan bukatar horar da ma’aikatanta (NYSC’s) kan sanin ya kamata.

Shugaban cibiyar nazarin jagoranci da hadaddun ayyukan soji na NDA, Dokta Ben Audu, shawara ga darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed, ya ce horon ya zama dole, tare da la’akari da kalubalen da ke tattare da sarrafa albarkatun dan adam a wuraren aiki.

Audu ya shawarci NYSC da ta siya wannan ra’ayin saboda sakamakonsa zai bayyana ta hanyar inganta ayyukan ma’aikata.

Da yake mayar da martani, Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed ya yi maraba da shawarar, inda ya bayyana cewa horon wata hanya ce mai kyau ta inganta kwazon ma’aikata don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Don haka ya umurci sashen Tsare-tsare, Bincike da kididdiga da kuma tawagar daga NDA da su tsara hanyoyin da za a fara horon.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *