Take a fresh look at your lifestyle.

JAN HANKALI GAME DA KIDAYA TA 2023

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 280

Cikin shirye-shiryen gudanar da kidayar jama’ar da ke da kudirin ganin duk dan Najeriya an kidaya shi don samar da tsare-tsare na gudanar da harkokin gwamnati da kula da harkokin rayuwar al’umma da suka hada da lafiya da tsaro da samar da ababen more rayuwa da dai sauransu.

 

A wannan Alhamis babban darakta a hukumar wayar da kan jama’a ta kasa a Najeriya NOA Dr. Garba Abari ya wakilci ministan yada labaran da al’adu a ziyara zuwa birnin na Kano inda ya ziyarci fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero anan ne yace masu rike da sarautun gargajiya na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen fadakar da al’umma kan muhimmancin kidayar ta mutane da gidaje ta 2023. Shi kuwa wakilin mai martaba sarkin na Kano kuma Madakin Kano Alhaji Yusif Nabahani ya ba wa kwamitin tabbaci na samun goyon baya don samun nasara. A can dakin taro na Meena kuwa a birnin na Kano wakilin ministan Dakta Abari yace dalilin kafa kwamitin nasu shine a wayar da kan al’umma kan muhimmancin kidayar jama’ar don samar da ci gaba ga kasa.Ya kuma bayyana dalilin kwamitin nasu zuwa Kano:

 

“ Na farko muyi tuntuba ga al’ummar jihar ta Kano saboda wannan muhimmin abu da zai faru a kasa wato kidayar jama’a da gidaje, na biyu a wayar wa al’umma kai abubuwa da ake fada game da kidayar wadanda ba na gaskiya ba, na uku mu saurari al’umma duk abin da ya shige masu duhu a wayar masu da kai, na hudu mu yi amfani da duk sassa da muka gayyata anan su isar da sako ta hanyar kafofin sadarwarsu don isar da sakon ga jama’a.”

 

Muhammad Garba kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida a Kano shine shugaban yada labarai na wannan kwamitin a Kano da yake nasa jawabi ga manema labarai a yayin zaman zauran tuntubar ya bayyana cewa kidayar jama’a na da muhimmancin gaske musamman ga al’ummar jihar ta Kano wacce a tsawon lokaci take ja-in-ja da jihar Legas a yawan jama’a:

 

“Jihar Kano tafi kowace jiha a Najeriya yawan jama’a, dama jihar Legas ce muke ja suna ja amma wannan karo in Allah Ya so za mu tabbatar masu da cewa Kano ce kan gaba. Abu muhimmi shine mutane su fahimci cewa kidaya ba zabe ba ce kada a siyasantar da batun.”

 

Da yake nasa tsokaci a wajen taron shugaban gidan rediyon Muryar Najeriya VON Mista Osita Okechukwu ya bayyana cewa kidayar jama’a ba zabe bace abu ne da ke da muhimmanci ga kowa:

 

“Gwamnatin tarayya na son ta yi tsari mai kyau ga al’umma don samun ci gaba don haka kada ka bari a wuce ka yayin kidaya ka tabbatar an kidayaka, ba batu bane na siyasa da wata jam’iyya za ta so ta yi nasara. Wannan nasara ce ga kasa baki daya, ba gasa ba ce. Wadanda suke nan a wannan rana sune za a kidaya koda ‘yan Lebanon ne ko Masar Ko ‘yan Chaina ko Amurka duk inda suke a Najeriya za a kidaya da su. Kowane dan kasa za a kirga shi babu banbanciu na addini ko kabila.”

 

Sauran mambobi na wannan kwamitin wayar da kan al’umma kan kidayar ta 2023 sune shugabanni na kafafan yada labaran da suka hada da gidan rediyon Najeriya  FRCN da gidan talabijin na kasa NTA da Muryar Najeriya  VON da shugaban kungiyar ‘yanjarida ta kasa a Najeriya NUJ, da kungiyar editoci ta kasa wato Guild of editors da sauransu.

 

Wannan taro dai ya samu halartar kungiyoyi da suka hadar da na limaman addinin Islama da na Kirista da kungiyoyin mata da masu bukata ta musamman da masu yi wa kasa hidima da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *