Zababben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake jan hankali na masu rike da madafun iko a kananan hukumomi na jihar da su guji bari ayi amfani da su wajen wawashe kudaden da ke baitil malin kananan hukumominsu don daukar nauyin zabukan da ba su kammala ba a karshen makon nan, wato ranar 15 ga watan Afrilu 2023.
A jawabin da ya fitar ga manema labarai mai magana da yawun zababben gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce sun sami bayanai sahihai cewa: “Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta ba da umarni a saki kudi Naira miliyan 61 ga karamar hukumar Doguwa da sama da Naira miliyan 60 ga karamar hukumar Nasarawa da wasu miliyoyin daruruwa ga wasu kananan hukumomin don daukar nauyin zabukan da ba a kammala ba.”
Dawakin Tofa ya kara da cewa:” Wadannan kudaden za a yi amfani da su ne kawai don daukar nauyin batagari su tada hargitsi a hana zaman lafiya ga al’ummar Kano a lokacin zaben.
Don haka yayi gargadi ga shugabannin kananan hukumomi da manyan maaikatan da ke karkashinsu da suka hada da ma’aji-ma’aji da sauran jami’ai a matakin jiha da kananan hukumomin da ahir dinsu su bari a yi amfani da su wajen karkata dukiyar al’umma da sa ta inda bai dace ba. Har ila yau ya kara da cewa:” Muna yaba wa masu kishin jiha da suka ba da bayanan wannan almundahna, sa nan duk ma’aikaci da ya sake ya sa hannunsa a duk wata badakala ya tuhumi kansa sa’ilin da zai bayyana gaban shari’a.”
Zababben gwamnan ya kara da cewa: ” Mun samu bayanai an shigo da ‘yan daba wasu daga wajen jihar don wargaza zaman lafiya da aka samu a jihar don haka muna kira ga jami’an tsaro su yi duk mai yiwuwa don dakile shirin batagari. Idan kunne ya ji jiki ya tsira.”
Leave a Reply