Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta bayyana Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala ranar Asabar din nan na danmajalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada bayan da yayi nasara kan abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP Yusha’u Salihu Abdullahi .
Acewar baturen zaben Farfesa Sani Ibrahim: Daguwa ya samu kuri’u 41,573 yayin da Abdullahi ya samu kuri’u 34,831 a zaben da aka kammala.
Idan dai ba a manta ba a ranar 25 ga watan Fabrairu bayan kammala zaben shugaban kasa da ‘yanmajalisar tarayya an bayyana Doguwa da yin nasara sai dai daga bisani baturen zaben Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai yace sai an sake zabe a wasu tashoshin zabe sama da goma domin sakamakon da ya bayyana da fari an tilasta shi ne ya fada ba haka yake ba.
A canma karamar hukumar Fagge kammala zaben danmajalisar wakilan da aka yi sakamakon ya nunar da cewa Barista Muhammad Bello Shehu na jam’iyyar NNPP ya lallasa abokin takararsa na jam’iyyar APC Aminu Suleiman Goro.
Acewar jami’in bayyana sakamakon Farfesa Ibrahim Tajo Suraj: Shehu na jam’iyyar NNPP ya samu yawan kuri’u da suka kai 19,024 yayin da Aminu Goro ya samu kuri’u 8,669. “Barista MB Shehu na jam’iyyar NNPP, kasancewar ya cika ka’idoji da doka ta tanada ta hanyar samun kuri’u mafiya rinjaye anan ina bayyana shi a matsayin wanda ya lashe wannan zabe.” Bayanin Farfesa Suraj.
Leave a Reply