Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya rantsar da Mai Sharia Olukyode Ariwoola a matsayin mukaddashin Alkalin alkalan Najeriya .
An gudanar da gajeren bikin rantsuwar ne a ranar Litinin a zauren majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne suka shaida rantsuwar.
Wannan dai na zuwa ne bayan murabus din tsohon alkalin alkalan Najeriya mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad bisa dalilan rashin lafiya.
An haifi Mai shari’a Ariwoola wanda shi ne babban alkalin kotun koli a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1958.
A baya ya kasance Alkalin Kotun daukaka kara kafin a daukaka shi zuwa kujerar Kotun Koli.
ABDULKARIM
Leave a Reply