Zababben Gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi da al’ummar jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya murnar kammala azumin watan Ramalana.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu a ranar Juma’an nan, zababben gwamnan jihar ya yi wa al’umma fatan alheri tare da kira ga jama’ar Kano da su yi addu’ar Allah ya bai wa shugabanni a dukkan matakai damar gudanar da aiyukan da al’umma za su amfana, musamman sabbin shugabannin da za su fara aiki daga ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara.
Injiniya Abba Kabir ya ce da yardar Allah za su samar da kyakkyawan yanayi da al’ummar jihar ta Kano za su yi rayuwa cikin kyakkyawan yanayi na tsaro
Har ila yau ya bukaci al’umma da su kasance masu kishin kasa, masu son zaman lafiya tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban Kano da Najeriya baki daya.
A karshe zababben gwamnan yayi kira ga al’umma da su bi hanyoyi da suka dace da doka wajen gudanar da shagulgulan bikin sallar a kuma guji tukin ganganci da sunan murnar sallah.
Leave a Reply