Take a fresh look at your lifestyle.

BUKIN SALLAH: SHUGABA BUHARI YA GANA DA ‘YAN AJIN SHI

0 148

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan ajin shi na Makarantar Firamare da Sakandare a ziyarar da suka kai masa a Daura, Jihar Katsina ,domin taya shi murnar bukin sallar Layya.

Shugaban ya tambayi halin rayuwa, lafiyar su da ta iyalan su.

Sunyi adduo’I ga abokanan su da suka rasu,bayan haduwar da akayi a bara da wannan shekara.

Shugaba Buhari ya nuna jin dadin shi game da wannan haduwar zumunci,yana mai cewa “Ina tuna lokacin da rayuwar da mukayi lokacin kuruciya.”

Sun dai tattauna na tsawon lokaci na tuna baya yayin karatun su a makaranta.

Shugaban ya gode wa ‘ yan Ajin su a makaranta da suka karrama da mutumta shi kamar yadda aka saba.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *