Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABA BUHARI YA BUKACI KAFA KOTUN YAKI DA RASHAWA A AFIRKA

0 160

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada shawarar kafa kotun kasa da kasa da zai hukumta wadanda suka aiakata cin hanci da rashawa a Afirka.

Shugaba Buhari, ya bada wannan shawarar ce a babban taron shugabannin kasashen Afirka akan yaki da rashawa a Afirka,kuma ya bukaci shugabannin das u maida himma wajen yakar cin hanci da rashawa da kirkiro hanyoyin da zasu magance satar kudaden alu’ma.

Hakan na daga cikin kalaman shugaban a bukin ranar yaki da rashawa a Afirka.

Ya yaba wa Shugabannin Afirka a kokarin da sukeyi na shugabanci da kuma maida hankali akan hukumta duk wanda aka samu da laifi tare da kwace dukiyoyin da suka ajiye a kasashen waje.

“Masu girma Shugabannin Afirka dake halartar wannan taro,rashawa mummunan abu ne da yake bukatar hanyoyin da suka dace wajen yakar shi. Na sanya ido akan yaki da rashawa a Afirka kuma naga ci gaban da aka samu wajen dakile shi. Dole muci gaba da yakar shi domin ceto Nahiyar da al’umar da ke fama da wannan bala’i. 

“A Najeriya, anyi nisa wajen yaki da rashawa tun shekara ta 2015. An samu gagarumar nasara da kame,hukumta,kwace kadarori da kafa dokar yaki da rashawa.

“Ina da yakinin cewa an samu kalubale,saboda haka dole a kara kaimi wajen yakin. Misali sai mutane da maaikatan gwamnati sunyi taka tsantsan da bin doka da oda a kowane lokaci. Dole ne bangarori masu zaman kansu su kasance cikin wannan tafiyar yaki da cin hanci da rashawa.Kasashen waje kuwa su bada hadin kai a wannan tafiyar tare da kafa kotun aikata manyan laifuka,” a cewar shuba.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *