Dan takarar shugaban Najeriya karkashin tutar Jamiyyar New Nigeria Peoples NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanar da Bishop Isaac Idahosa a matsayin mataimakin shugaban kasa a zaben Shugaban kasa a shekara mai zuwa 2023.
Bishop Idahosa,danh asalin jihar Edo, Pasto ne a mijamiar God First Ministry, Lekki Ajah.
Mai shekaru 57 da haihuwa kwararre neda ya samu kwarewar Injiniyar Motoci a kwalejin Politeknik dake Kaduna. Da na dakta a fannin addinin kirista. Yana da mata da ‘ya’ya biyu.
Sanata Kwankwaso ya sanar da wannan zabinda yayi na Bishop Idahosa yayi ne bayan nazari akan mutane ;yan takara ashirin daya bincika na tsawon lokaci akan wanda zai zama mataimakin sh.
Dan takarar Shugaban kasa na NNPP yace : Na zabi bishop Idahosa ne saboda kyakwan zato da ake das hi akan shin a mutumin kirki da sannin makamar kalubalen mulkin jihar Najeriya,kuma nake ganin da wadannan halaye na dattako da aka sanshi das u ya nuna mani cewa abokin tafiya ne saboda rikon amanar shi,.Kuma zabin Bishop Idahosa shine zaben cikakken dan Najeriya mai nagarta ga matasa. A cewar shi.
Sanata Kwankwaso ya nuna jin dadin shi cewa mai tsoron Allah ne abokin tafiyar da zai yi aiki da shi wajen ci gaban kasa tare da kafa sabuwar Najeriya,inda adalci,daidaito,hada kai,tsaro da ci gaba sune burin Jamiyyar.
Ana sa ran gabatar da Bishop Isaac Idahosa ga ‘yan Najeriya ranar litinin 18 ga watan Yuli, 2022 a dakin taro na kasa da kasa dake babban birni, Abuja da misalign karfe 10 na safe.
LADAN NASIDI
Leave a Reply