Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisa Ta 10: Doguwa Ya Bayyana Ra’ayinsa Na Zama Kakakin Majalisar Wakilai

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 341

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado-Dogwua, ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar wakilai ta 10, zai yi duba ta hanyar aiwatar da shirin nan na farfado da tattalin arzikin Najeriya wato “Renewed Hope 2023-Action Plan for Better Nigeria” wanda zababben shugaban kasa Sanata Bola Tinubu ya kafa.

Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban majalisar wakilai ta 10 a Abuja.

Da yake zantawa da mamema labarai Jim kasan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Kakakin majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya ce zai yi dukkan Mai yiyuwa don karfafa goyon bayan majalisar da nufin tabbatar da aiwatar da shirye-shirye da manufofin gwamnatin da zabben Shugaban kasa Bola Tinubu zai jagoranta.

Da yake jawabi a kan burinsa, ya ce zai karfafa rawar da majalisun za su taka wajen samun wakilci mai inganci tare da maido da kwarin gwiwar jama’a da shiga harkokin mulki.

Wannan a cewarsa ta hanyar saukakawa, daidaitawa, da sa ido, da kuma tantance dabarun shigar da jama’a a harkokin mulki da kasuwanci na gwamnati.

A cewarsa, idan aka zabe shi shugaban majalisar, zai tabbatar da hadin kai da kuma huldar aiki tare a tsakanin bangarori uku na gwamnati.

“A yau a zauren majlisar tarayyar Najeriya a arewacin Najeriya kaf baba wanda shekarunsa na aiki ya kai nawa, babu wanda nake zato gogewarsa da cancansa da zama musanman idan ka duba tsarin jerin matsayi da na rike a matsayina na shugaban masu rijaye tun daga zango na takwas zuwa yau, da kwamitoci da na rike na aikin majalisa da suke da nasaba da majalisu na kasashen duniya ma ba Najeriya ba, wannan ina ganin ya bani kyayyawar dama da idan ‘yan’uwana yan majalisa sun amince ya kamata su yadda su ara min dama ya zama nine zan shugabanci majalisa ta 10 idan ka duba dukkan wadannan abubuwan da na fada”. In Ji Ado Doguwa

Shugaban masu rinyayen majalisar ya kara da cewa, zai tabbatar da cewa majalisar ta gudanar da harkokinta cikin gaskiya da rikon amana, inda kowane dan majalisar zai kasance da alhaki tare da bin diddigin al’ummar da yake wakilta.

Dan gane da batun Mika kujerar ga wata shiyya kuwa, Shugaban masu rinyayen ya ce a shirye yake ya yi biyayya ga Jam’iyya a duk lokacin da ta ayyana yankin da za a tura kujerar Kakakin Majalisar ta Wakilai.
“Jam’iyya za ta same ni mai biyya, za ta same ni mai girmamawa da mutantan dukkan tsarin da ta zo da shi don aiwatar da kuma zatar da yadda take so a bada shugabanci na majalisar tarayyar Najeriya ta kuma majalisar kasa baki daya”

Shi ma da yake tofa albarkin bakinsa Hon injiniya Sani Bala daga Jihar Kano ya yayyana cewa Dogowa shi ya fi cancanta ya zama Kakakin Majalisar.
“Babban dalilin da ya sa muka mara masa baya saboda muna ganin babu wanda ya fi shi cancanta a cikin dukkan yantakarar nan goma da suka fito. Na farko babu wanda ya fi shi sanin harkar majalisa saboda shi ya fi su dadewa a majalisar. Na buyi kuma ya iya mu’amala da mutane, ya san dokokin majalisa ya san kuma tsarin majalisa”.In Ji Hon. Sani Bala

Shi kuwa Hon Samila Sulaiman daga jihar Kaduna kira ya yi ga zabbabbun Yan Majalisar da su mara masa baya.

“A irin salon na shugabanci na Hon Alasan Ado Doguwa, mutunta yan majalisu yan uwansa, da fida al’umma ayi tafiya bai daya da yake da shi tsakaninshi da ‘yan majalisu, yan majlisu sababbi masu zuwa da manya manya na kasa da al’uma na kasa da tsakiya da na sama za su bashi dukkan goyan da ake bukata”. In ji Hon Samaila Sulaiman

Kimanin Yan majalisu goma ne yanzu haka suke zawarcin kujerar ta Kakakin Majalisar Wakilai wadanda suka fito daga shiyyoyi daban daban na Najeriya.

Ga Wakilin Muryar Najeriya a Majalisar Dokoki Abdulkarim Rabiu dauke da cikakken rahoto:

 

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *