Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari ya taya Gwamnan Filato murnar cika shekaru 60 a Duniya

0 113

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a yayin bikin cikarsa shekaru 60 da haihuwa, yana mai nuna jin dadinsa kan dimbin soyayyar da gwamnan da al’ummar jihar Filato suka nuna masa.

 

 

A cikin sakon ya ce: “Ina mika godiyata ta musamman ga Gwamna Lalong a daidai lokacin da yake murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Na gode da amincewar da kuke da ita a cikin abokantakarmu.”

 

 

Shugaba Buhari ya yabawa Gwamna Lalong bisa ayyukan da ya yi tun bayan rantsar da shi da kuma hukunce-hukuncen da ya dauka cikin shekaru takwas da suka wuce, Shugaba Buhari ya ce:

 

 

“Wadannan suna nuna tasirinsa a matsayinsa na jagora. Dangane da harkokin tsaro da jin dadin jama’a, Gwamna ya zama abin koyi ga kasa baki daya. Na yi imanin makoma mai girma tana gabansa.”

 

 

Da yake yi masa fatan alheri cikin shekaru masu zuwa, Shugaba Buhari ya bukaci Gwamna Lalong da ya ci gaba da kawo sauki da mutunta al’ummar jiharsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *