Take a fresh look at your lifestyle.

HYPPADEC: Shugaban ALGON a Jihar Neja na son a karawa hukumar HYPPADEC kudaden gudanar da ayyukanta.

Nura Muhammed,Minna.

0 274

Shugaban karamar hukumar Borgu a jahar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya kana shugaban chayamomin jahar ALGON a turance  Honorable Sulaiman Yarima ya bukaci yan majalisun taraya da su karawa hukumar kula da jahohin dake Samar da wutan lantarki ta ruwa kasafin kudin da ake basu domin cigaba da aiwatar da ayyukan raya kasa a jahar Neja.

 

 

Honorable Sulaiman Yarima ya bukaci hakan ne a wajan taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta HYPPADEC ta shirya domin wayar da kan alumma don sanin hanyoyin kare kai daga  ambaliyar ruwa a wannan shekarar da muke ciki.

 

 

Honorable Sulaiman Yarima ya ce hukumar ta HYPPADEC na shinfida manyan ayyukan raya kasa a jahohin dake karkashin kulawarta a don haka akwai bukatar ganin an kara mata kudade a  kasafin kudinta duba ga irin yadda take aiwatar da ayyuka a yankunan da ke fama da ambaliyar ruwan da ya yi sanadiyar barnata anfanin gona da gidaje da sauran mahimman abubuwa na alumma.

 

 

Har ila yau shugaban karamar hukumar Borgu ya shawarci hukumar ta HYPPADEC da sauran masu ruwa da tsaki da su sake duba sauran matsalolin da alumma ke fuskanta domin kawo masu agaji baya ga ambaliyar ruwa.

 

 

Yarima ya Kara da cewar akwai batun ilimi da tsaro da yanzun haka Shuwagabanin kanannan hukumomin dake jahar Neja ke fadi tashin ganin sun magance su, a don haka ya ce akwai bukatan  ganin hukumar ta HYPPADEC da kanannan hukumomi  sun hada  hannu domin kawowa alummar jahar cigaba.

 

 

A jawabin sa shugaban hukumar ta HYPPADEC Alhaji Sadiq Yalwa ya ce hukumar ta tsara yadda zata wayar da kai da kuma taimakwa alummar jahohin da ke karkashinta domin sanin irin illar ambaliyar ruwa da Kuma yadda zasu kare kansu daga shiga hadarin.

 

Sadiq Yalwa ya ce hukumar ta HYPPADEC a ko da yaushe a shirye take ta hada hannu da Shuwagabanin kanannan hukumomi 17 da ambaliyar ruwa ta shafa a jahar Neja a shekarar da ta gabata domin sanin yadda za a bi wajan ganin ba a sake shiga matsalar ba a wannan shekarar da muke ciki.

 

A dai taron na masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya akwai hukumomin bada agajin gaggawa da suka hada da NEMA da NISEMA da suka halarci taron, sun kuma nuna sha’awarsu na hada hannu da hukumar ta HYPPADEC domin samar da yanayi mai kyau ga alummar jahar Neja da sauran jahohin dake karkashin kulawarta.

 

 

Nura Muhammed,Minna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *