Take a fresh look at your lifestyle.

IBB University: Jami’ar jihar Neja ta Kori dalibai 24 bisa laifuffuka daban daban.

0 261

Jami’ar  jahar Neja dake  arewa ta tsakiyar Najeriya ta shirya karrama mutun hudu da digirin digirgir a bikin yaye dalibanta  da za a  yi a ranar Asabar 20 ga wannan watan na Mayu.

 

 

Shugaban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, professor Abu Kasim Adamu shine ya bayana haka ga manema labarai gabanin shirye shiryen jami’ar na yaye dalibai 6,154

 

 

Professor Abu Kasim Adamu ya ce daliban sun hada da na shekarar karatu na 2019/2020 da Kuma na 2021/2022 inda 5,719 suka kasance masu karatun digiri na farko yayin da aka sami dalibai 435 dake karatun digiri na biyu da na uku a cikin wadannan shekarun.

 

 

Shugaban jami’ar ya kara da cewar bisa al’ada jami’ar ta tsara karama wasu fitattun yan Najeriya daga sassan kasar daban da suka hada da gwamnan jahar Plato Simon Bako Lalong da  za a karrama da digirin digirgir kan Shugabanci sai tsohon gwamnan jahar Kano kana shugaban kamfanin mainstream energy Col Sani Bello Mai murabus da za a karrama dagirin digirgir, sai Malam Ibrahim Aliyu shugaban kungiyar Aliyu Foundation inda Shima zai karbi digirin digirgir da Kuma shugaban kamfanin BUA group Alhaji Abdulsamad Isiyaka Rabiu da shima zai karbi digirin digirgir a bikin yaye daliban na jami’ar jahar Neja.

 

 

Professor Abu Kasim Adamu ya ce an sami dalibai da suka sami sakamako mai kyau na matakin ajin farko wato  first class su 37 sai mataki  na biyu wato second class upper su 954 inda kuma aka sami mataki na uku su 3,293 second class lower sai  Kuma a matakin karshe na yan third class aka sami dalibai 1,538.

 

 

Shugaban jami’ar ya kara da cewar gwamnatin jahar karkashin Shugabancin gwamnan jahar Abubakar Sani Bello ta himmatu wajan ganin jami’ar ta warware manyan matsalolinta na kudi da take fama da su, inda a baya gwamnatin jahar ta gina dakunan kwanan dalibai da nufin kawo sauki ga daliban dake karatu a jami’ar.

 

 

Professor Kasim Adamu ya ce  ” Wannan babban cigaba ne na yadda gwamnan jahar ke fadi tashin ganin an dai daita alamura a jami’ar jahar , Muna fatan Kuma sabuwar gwamnati zata cigaba daga inda aka tsaya domin ciyar da jami’ar da ilimi gaba a jahar Neja”

 

 

Professor Abu Kasim Adamu ya ce jami’ar ta sallami wasu daga cikin daliban jami’ar wadanda suka karya ka’idojin da dokokin jami’ar na rashin kokari  da Kuma nun rashin da’a.  Inda ya ce an kori 17 daga cikin daliban da aka kama da aikata laifuffuka na  rashin da’a da shiga kungiyoyin da hukumar makarantan ta haramtawa dalibai shiga,  ta kuma sallami 7 daga cikin su wadanda suka kasa katabus a karatu.

 

 

Nura Muhammed,Minna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *