Babban hafsan sojin kasar Sudan Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kori mataimakinsa kuma dakarun Rapid Support Forces, RSF, kwamandan Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Dukkaninsu Janar Burhan da Hemedti sun yi aiki a matsayin shugaba da mataimakin majalisar mulkin soji, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban 2021.
A wata doka da aka fitar ranar Juma’a, Janar Burhan ya nada tsohon madugun ‘yan tawaye, Malik Agar a matsayin mataimakinsa. Mista Agar kuma memba ne na Majalisar Sarauta.
“Ya umurci sakatariyar Majalisar Sarauta da hukumomin jihar da su gaggauta aiwatar da dokar.”
A watan jiya ne dai hafsan sojojin ya rusa RSF tare da ayyana mayakansa a matsayin ‘yan tawaye bayan da aka gwabza fada tsakanin dakarun da ke gaba da juna.
Tuni dai kasar ta fada cikin fadace-fadace da tashe-tashen hankula.
L.N
Leave a Reply